Zariya


















Zariya (Ko kuma da turanci Zaria, sai kuma Zazzau sunan da ake mata lakabi da shi). Zariya gari ne dake a cikin arewacin Najeriya, kuma karamar hukuma ce a jahar Kaduna, tana da iyaka da Funtuwa, babban birnin Kaduna, da kuma Igabi duka a cikin ƙasar Najeriya. A bisa ga ƙidayar jama'a na shekara ta dubu biyu da shidda (2006), jimillar mutane dubu dari bakwai da sittin (700060) ne a garin Zariya, to amman daga bisani an kimanta yawan su a shekara ta dubu biyu da sha bakwai (2017), ga jimillar mutane miliyan daya (1000000). Birnin Zariya tana da kilomita ɗari biyu da sittin (260kms), ne daga garin Abuja, kilomita tamanin (80kms) ne daga Zariya, kilomita dari daya da sittin (160), ne daga Kano.[1] Garin Zazzau an saka masa suna ne daga Sarauniya Amina.[2]
Tarihi Akkan zariya.
[gyara sashe | gyara masomin]Asalin sarakunan zariya Hausawa ne dasu ke mulkan su, wadanda su kayi sarauta tun daga shekara ta dubu ɗaya da ɗari biyar da biyar (1505), zuwa shekarar dubu daya da ɗari takwas da biyu 1802, A shekara ta dubu ɗaya da ɗari takwas da hudu 1804, ne Shehu Usman ɗan Fodiyo yayi jihadi, inda ya yaƙi sarkin gobir mai suna Yunfa, a Yakin kwoto, daga nan ne ya fara yaɗa sarautarsa da musulunci zuwa masarautun Hausawa, A garin zariya kuma akwai Malam Musa wanda ya daɗe yana da’awar zuwa ga addinin musulunci, Malam Musa Bafillatani ne, Jin Jihadin Usman ɗan Fodiyo yasa shima ya karɓi tuta daga Usman ɗan Fodiyo. Da Malam Musa da Yamusa mutumin fulanin Barno suka doso Zariya suka yaƙi sarki Makau ɗan kabilar Hausawa, Makau sai ya gudu shi da mutanensa zuwa Zuba, wani gari ne na Gwari da Koro a yankin Abuja a yau, Malam Musa sai ya zama Sarkin zazzau na farko daga ƙabilar Fulani, bayan rasuwarsa sai aka naɗa Yamusa a shekarar ta dubu ɗaya da ɗari takwas da ashirin da ɗaya 1821, a matsayin sarkin zazzau, shi kuma fulanin Barno ne, daga nan ne Bare-Bari da Fulanin Mallawa suka fara sarauta a kasar zazzau.[3] (Ihayatu (talk) 21:14, 30 Mayu 2023, (UTC)).

Birni ne a ƙasar Hausa wanda kuma yana ɗaya daga cikin garuruwan da Shehu Usman ya bada tutar addinin musulunci ya tabbata a ciki. Birni ne mai ɗadin zama saboda yanayinsa gashi kuma babbar cibiyar ilimin addini dana boko a arewacin Najeriya. Wannan gari Allah ya albarkace shi da kasa ta noma da kuma ilimin addinin musulunci dana zamani wanda a dalilin haka ne baki daga maƙotan garin suke zuwa domin neman ilimi kai harma da na ƙasashen waje da kuma mutanen garin Zariya su kansu, Waɗannan garuruwa a wancen lokacin duka suna karkashin mulkin garin Zazzau ne, inda Zariya take a matsayin babban birni, amman yanzu wasu daga cikin waɗannan garuruwan basa ƙarƙashin zazzau.[3] (Ihayatu (talk) 21:14, 30 Mayu 2023, (UTC))
| s/n | Garuruwa | Garuruwa | |
|---|---|---|---|
| 1-2 | Anchau | Zaria | |
| 3-4 | Soba | ||
| 5-6 | Damo | Likoro | |
| 7-8 | Ɗan Alhaji | Igabe/Igabi | |
| 9-10 | Garu | Ikara | |
| 11-12 | Gimba | Zuntu | |
| 13-14 | Giwa | Richifa | |
| 15-16 | Fatika | Kargi | |
| 17-18 | Funkwi | Kauru | |
| 19-20 | Ɗan Maliki | Lere | |
| 21-22 | Durum | Kubau | |
| 23-24 | Ɗan Lawal | Kudan | |
| 25-26 | Faki | Kuadaru |
Mutane.
[gyara sashe | gyara masomin]Asalin mulkin Zariya yana ƙarkashin Sarakunan Hausawa ne, ana kiran garin da zazzau, zakzak ko zegzeg, dukkan waɗannan sunayen ana kiran garin Zaria da shi, amman daga bisani sunan zazzau ya canza zuwa Zariya, A inda kuma sarautar aka fi kiranta da zazzau, shiyasa sarkin garin ake kiran shi da sarkin zazzau, mutanen da suka fito daga garin ana kiransu da suna Bazazzagi, jam’i kuma Zazzagawa.[3]. (Ihayatu (talk) 21:14, 30 Mayu 2023, (UTC))
Sarauta.
[gyara sashe | gyara masomin]Asalin mulkin Zariya tana ƙarƙashin Sarakunan hausawa ne, waɗanda ke mulkan masarautan Zazzau, amma daga baya sarakunan Mallawa da fulani suka haɗa hannu da karfi suka yaƙi sarakunan hausawa a shekarar 1804. Sarakunan Hausawa na farko sun rayu ne a ƙarni na 15, waɗanda a wannan lokacin ba'a iya tina shekarun da sukayi sarauta, amman sarakunan hausawa na biyu sunyi mulki ne a ƙarni na 16, inda aka taskace shekarun mulkin su, har zuwa lokacin da sarakunan Fulani suka yaƙe su, sarkin su na ƙarshe shine Makau a Zariya, a Gobir kuma shine Yunfa.
| s/n | Sarakuna | Shekara |
|---|---|---|
| 1 | Gunguma | |
| 2 | Matazo | |
| 3 | Tumsah | |
| 4 | Tamusa | |
| 5 | Suleimanu | |
| 6 | Maswaza | |
| 7 | Ɗinzaki | |
| 8 | Nayoga | |
| 9 | Kauchi | |
| 10 | Nawainchi | |
| 11 | Machikai | |
| 12 | Kewo | |
| 13 | Bahikarr | |
| 14 | Majidada | |
| 15 | Dahirahi |
| s/n | Sarakunan Hausa | Shekara |
|---|---|---|
| 1 | Moman Abdu | 1505 – 1530 |
| 2 | Gudan Dan Masukanan | 1530 – 1532 |
| 3 | Nohirr | 1532 – 1535 |
| 4 | Bakwa Turunku | 1535 – 1536 |
- Babbabn Kofar Fada na garin Zaria
Arziki.
[gyara sashe | gyara masomin]Masana'antu
[gyara sashe | gyara masomin]Garin Zariya an san su da sana’o’i daban daban, Garin jere da kajuma suna karkashin Zariya, sun yi suna akan saka ta hannu.[4] Abu mai muhimmancin gaske a kasar Zariya shine Audiga, wanda ake diba daga Zariya da kano zuwa kasashen turawa domin amfanin masana’antu, garin Zariya sun shahara da sakan kayan sakawa, hula, da kuma rini.[5]
Kasuwanci
[gyara sashe | gyara masomin]Zariya gari ne, na kasuwanci da harkar noma.
Noma
[gyara sashe | gyara masomin]Allah ya ba Zariya kasar noma mai kyau.ana noma masara, doya, dawa, dauro, Gero, rake, barkono, shinkafa, dss.
Sufuri
[gyara sashe | gyara masomin]Zariya suna da hanyar sufurin jirgin ƙasa da hada Zariya da garuruwan Lagos , Kano, Abuja da kuma Kaduna (birni).[6][7]
Ilimi.
[gyara sashe | gyara masomin]Zariya cibiya ce ta ilimin addini da boko, a garin ne jami'ar Ahmadu Bello ta ke, bayan ABU akwai makarantun Ilimi kusan Tara 9 a cikin garin Zariya.Kamar; 1. Federal College of Education ((F.c.e)). 2. Nuhu Bamalli Polytechnic. 3. Ameer Shehu Idris. 4. National Institute of transport Technology((Nitt)). 5. Leather Research. 6. Narict 7. National College of Aviation((Ncat)). 8. Napri 9. Institute of Animal research((I.A.R)). Akwai kuma malaman addinin Musulunci manya kaman; 1. Sheikh Mua'azu 2. Sheikh Abdulkadir 3. Sheikh Yahuza.
Da dai sauran su.
Addini.
[gyara sashe | gyara masomin]Musulunci
[gyara sashe | gyara masomin]Mutanen Zariya ma fi yawancinsu mabiya addinin Musulunci ne.
Kiristanci
[gyara sashe | gyara masomin]Kasantuwar ma'aikatu na Gwamnatin tarayya a garin Zariya da kuma hanyoyin sufuri da yanayin kasuwanci a garin, hakan ya sa mabiya addinin Kiristiyaniti na kara yawa a garin.
Masana'antu.
[gyara sashe | gyara masomin]Akwai masana'antu kamar su "Sunseed", Pz, dasau ransu.
Garuruwa.
[gyara sashe | gyara masomin]A lokutan a garin Zariya akwai Ganuwa, amma daga baya duk an cire su.[8][9]
- Taswiran dake nuna garin Kaduna da yankin Zaria
Bibiliyo.
[gyara sashe | gyara masomin]- Professor lavers collection: Zaria Province, Arewa House.
- Maiwada, Salihu and Renne, Elisha P. (2007) "New Technologies of Embroidered Robe Production and Changing Gender Roles in Zaria, Nigeria, 1950–2005"
- Gihring, Thomas (1984). "Intraurban Activity Patterns among Entrepreneurs in a West African Setting". Geografiska Annaler. Series B, Human Geography.
- Smith, Michael G. (1960), Government in Zazzau 1800–1950 International African Institute by the Oxford University Press, London, OCLC 293592; reprinted in 1964, and 1970.
- Dan Isaacs (28 September 2010). "Nigeria's emirs: Power behind the throne". BBC News. Retrieved 29 September 2010.
Diddigin bayanai na waje.
[gyara sashe | gyara masomin]- Fayal masu alaqa da Zaria a commons.wikimedia.org
- Asalin tushe
Manazarta.
[gyara sashe | gyara masomin]
- ↑ http://www.britannica.com/eb/article-9078266/Zaria
- ↑ https://www.britannica.com/place/Zaria-Nigeria
- 1 2 3 professor lavers collection: zaria province.
- ↑ Maiwada, Salihu and Renne, Elisha P. (2007) "New Technologies of Embroidered Robe Production and Changing Gender Roles in Zaria, Nigeria, 1950–2005" Textile History 38(1): pp. 25-58, page 25
- ↑ Gihring, Thomas (1984). "Intraurban Activity Patterns among Entrepreneurs in a West African Setting". Geografiska Annaler. Series B, Human Geography. 66 (1): 19–20.
- ↑ https://www.bbc.co.uk/news/world-africa-21364541
- ↑ https://www.economist.com/news/middle-east-and-africa/21571481-renovated-railway-line-welcome-more-are-still-sorely-needed-slow
- ↑ https://web.archive.org/web/20091027035909/http://www.abu.edu.ng/bsn/zaria.php
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2009-10-27. Retrieved 2020-12-27.